A yau Litinin Shugabanni daga yankin gabashin Afrika na yunkurin su ga cewa gwamnatin Sudan ta Kudu da ‘yan tawayen kasar, sun saka hanNu a shirin samar da zaman lafiya, domin kawo karshen yakin basasan da aka kwashe watannin 20 ana yi a kasar.
Shugaba Salva Kiir da abokin hamayyrasa Riek Machar, suna halartan zaman da ake yi yanzu haka a Addis Ababa, wanda ke samun jagorancin kungiyar kasashen gabashin Afrika ta IGAD.
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya saka hotunanan Shugaba Kiir da Machar a shafinsa na Twitter, yayin da suke halartar taron a jiya Lahadi.
Hakan na faruwa ne yayin da ake kokarin a kaucewa cikar wa’adin da aka shata na yau Litinin ba tare da an samu matsaya kan yadda za'a kawo karshen rikicin ba.
Wannan zaman tattaunawa dai na gudana ne hade da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.
Shugaba Kiir ya halarci taron ne, kwanaki biyu bayan da ya ayyana cewa ba zai je kasar ta Habasha ba saboda a cewar shi, ‘Yan tawayen sun rabu zuwa gida biyu.