Yayinda yake jawabi a wurin bude taron alkalan Najeriya na shekara shekara, Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ce samamen da aka kai gidajen wasu alkalai da aka kama aka kuma gurfanar dasu a gaban kuliya ba a yi hakan da nufin cin mutucin su ba ne.
Shugaba Buhari ya kara da cewa wancan matakin da suka dauka ba kutse suka yiwa bangaren shari’a ba ko kuma kaskantar da alkalan kamar yadda wasu kafofin yadda ke ta yayatawa.
Shugaban ya yi ga kira alkalan da su fito da tsare-tsaren da zasu sa su gaggauta yanke hukunci ga wadanda ake zargi ake kuma tsare dasu a gidajen kaso. A cewar shugaban a watan jiya ya rubutawa gwamnoni, wasikar cewa su kai ziyara zuwa gidajen kaso da manyan alkalansu su sake bayin Allahn da ake tsare dasu ba tare da aikata wani laifi ba.
Akan alaka dake bangaren zartaswa da na shari’a masanin shari’a Dr Mainasara Kogo Ibrahim yayi tsokaci a kai. Yace alkalai na ganin ba daidai ba ne a kai samame gidajen alkalai har a gurfanar dasu gaban kuliya. Yace haka ma akwai kuskure a bangaren zartaswa saboda kwana kwanan nan hukumar DSS ta ki mika wa hukumar EFCC wani jami’inta domin a bincike shi kamar yadda EFCC din ta bukata. A wasu lokutan ma gwamnati ta kan ki bin hukuncin kotu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5