Gwamnar Tokyo Ta Yi Gargadi Kan Yiwuwar Sake Bullar COVID-19

Gwamnar Tokyo, Yuriko Koike

Gwamnar Tokyo Yuriko Koike ta fitar da wata sanarwar gargadi a birnin game da yiwuwar sake bullar cutar coronavirus.

Sanarwar da aka fitar a jiya Talata na zuwa ne bayan da aka sami rahoton mutum 34 sun kamu da cutar ta COVID-19, adadi mafi yawa da aka taba samu a wata guda.

Hakan na faruwa ne ‘yan kwanaki bayan da aka dage dokar ta bacin da aka sanya a birnin.

Mutane kalilan ne aka samu rahoton sun kamu da cutar a karshen watan Mayu da ya gabata.

Ko da yake ta ce ba ta da shirin sake fitar da gargadin da ya shafi baki dayan birnin a hukamace amma ta ce idan adadin masu kamuwa da cutar ya ci gaba da karuwa har ya kai akalla mutum 50 a rana, to za ta sake ba da umurnin rufe masana’antu.

Yuriko ta ce ta na kyautata zaton bude gidajen raye-rayen ‘yan Japan, kamar na Karaoke su ne suka janyo sabbin kamun cutar.