Gwamnonin da Suka Bar PDP Sun Yi Kuskure

Wasu gwamnonin da suka yi tawaye

Masu harsashen kan harkokin siyasa aNajeriya suna ganin gwamnonin da suka bar jam'iyyar PDP sun yi kuskure.
Cikin gwamnoni bakwai da suka yiwa jam'iyyar PDP tawaye a karkashin shugabancin Alhaji Kawu Baraje biyar sun kulla kawance da sabuwar jam'iyyar APC da nufin narkewa cikin jam'iyyar.

To sai dai wasu suna ganin wadannan gwamnonin sun tafka wani mugun kuskure. Masu amanna da tasirin PDP sun ce sun yi batar basira. Tsohon Sanato Abubakar Gire ya ce ba za'a sake wata jam'iyya da zata kawar da tasirin PDP ba a wannan zamani. Ya ce jam'iyyar PDP kusan ita ce kadai jam'iyya a Najeriya. Kowa bukatarsa ce ya shigo PDP ya zama wani abu a Najeriya. Ya ce kasar nada mutane miliyan dari da saba'in kowa yana son ya biya bukatarsa a cikin jam'iyyar. Don haka dole ne a samu irin wannan hayaniyar.

Dangane da tasowar jam'iyyar APC Sanato Gire ya ce PDP bata girgiza ba. Idan wani abu ya raunana PDP to 'yan PDP din ne suka raunanata. Ya ce babu wata jam'iyya da zata fito ta kwace mulki a hannun PDP tun daga kananan hukumomi har zuwa gwamnatin tarayya idan ba 'yan PDP sun yadda ba.Yace idan aka dauki matakan da suka dace PDP zata sake darewa kan mulkin kasar a zabe na gaba.

Wata tsohuwar 'yar siyasa Binta Kuraye ta ce gwamnonin da suka fice tamkar sun je sun shiga gidan haya ne. Ta ce duk wanda ya bar gidan iyayensa ya je gidan wasu to zai hadu da wulakanci. Wanke wanke zai shiga yi. Ta ce barin PDP ba shi ne zai kawo sulhu ba kuma ba shi ne zai sa su ji dadin abun da suka yi ba.

To sai dai dan siyasar adawa mai akidar nehu Dr Mohammed Junaidu ya ce kaucewa daga tafarkin gaskiya ke wahalar da 'yan siyasar Najeriya.Ya ce abun da ya sa aka samu baraka muna-muna da ake son ayi dasu ya jawo hakan . Ya ce kowa ya san ba mai iya cin zabe idan ba'a hada da gwamnoni da 'yansanda ba. Su gwamnonin kudaden kananan hukumomi suke anfani da shi da na jama'a. Abu na biye da wannan shi ne karya yarjejeniyar da aka yi da shugaba Jonathan. Da shugaba 'Yar'Adua ya rasu an ce ya yi shugabanci sau daya kana ya mika ma wani a cigaba da shirin karba karba. Idan yana da mutunci kuma ba son yake ya zubar da mutuncinsa ba to ya kamata ya amince da shirin karba karba. Ya ce irin wannan ne Obasanjo ya so ya yi da ya gagara. Ya ce su kuma gwamnonin suna da nasu burin. Akwai wanda yake son ya yi shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa.

Saleh Shehu Ashaka nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnonin Da Suka Bar PDP Sun Yi Kuskure-3.01