Gwamnan Zamfara Ya Musanta Zargin Yin Zarmiya da Kudaden Jama'a

Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

Makon jiya ne aka ce hukumar EFCC ta bankado wata munamuna inda aka ce shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Zamfara yayi anfani da kudi har dalar Amurka miliyan uku wajen gina wani otel mai dakuna dari a wata anguwar masu hannu da shuni a Legas

Shugaban kungiyar gwamnoni Najeriya kuma gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari yayi taro da manema labaru inda ya karyata zargin da wasu kafofin yada labarai suka yi masa bisa ga wasu bayanai da aka ce hukumar EFCC ta fitar cewa ya gina wani katafaren otel a Legas da kudi dalar Amurka miliyan uku daga kudaden nan na Paris Club.

Gwamnan yayi karin haske akan zargin wanda ya hada da cewa wai har an mayar da zunzurutun kudi N500m da aka ce wani na hannun damansa yayi.

A cewar gwamnan kudi masu yawa haka ba daukansu a keyi ba a kaisu wani daki a ajye. A banki ake kaiwa walau Babban Banki ko banki na huldar yau da kullum. Yakamata kuma ace akwai asusun da kudi suke shiga ko suke fita.

"Na farko zan yi mamaki kwarai da gaske da za'a ta'llaka cewa irin an nade kudi kimanin dala miliyan uku na gina otel. Dole kudin nan zasu fito daga asusu ne, ko nawa ko na wani ko kuma na abokina" inji Gwamnan Yari.

Lokacin da gwamnan ya ji labarin wadda wata jarida daga kudu maso yamma ta buga tana zargin wani gwamna da gina otel din shi Gwamnan Zamfara ya dauka gwamnan da ake zargi daga shiyar ya fito. Sai gashi kwatsam an ambaci sunansa.

Gwamnan yace yayi mamaki da zargin saboda shi a cewarsa ko fili bashi dashi a koina a jihar Legas.

Gwamnan Yari yace cikin matakan da ya dauka shi ne garzayawa zuwa kotu domin shigar da karar hukumar EFCC da jaridar da ta watsa labarin domin su bayyanawa duniya inda otel din yake da inda ya fitar da kudaden ginashi kuma da wanda ya ba kudin. Yace musanta zargin da yayi bai isa ba kotu ce zata raba.

An ce masa idan an gudanar da bincike dangane da kudaden ba za'a sameshi da laifi ba, sai gwamnan yace inda ya fito sun fi daukar girman inda Allah ya ajiye mutum fiye da kudi. Ya kara da cewa inda ya fito basa bautawa kudi.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Zamfara Ya Musanta Zargin Yin Zarmiya da Kudaden Jama'a - 4' 49"