Gwamnan Yobe Ya Ce Sakacin Sojoji Ne Ya Yi Sanadiyar Sace 'Yan Matan Dapchi

  • Haruna Dauda Biu

Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe ya yi imanin cewa janye sojoji daga garin Dapchi ya taimaka ma 'yan Boko Haram sace 'yan matan makarantar kamar abun da sojoji suka yi a shekarar 2014 inda kwana guda da janyewa daga Bunu Yadi 'yan ta'ada suka kai hari makarantar gwamnatin tarayya suka hallaka dalibai 50 tare da yiwa makarantar kaca-kaca

Wata takaddama na kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Yobe da sojojin kasar dake samar da tsaro a arewa maso gabashin kasar akan yadda aka sace 'yan makarantar mata ta garin Dapchi makon jiya.

A karshen makon da ya gabata gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam ya zargi sojojin da yin sakaci, lamarin da ya taimaka aka sace daliban.

Inji gwamnan mako guda da janye sojojin daga garin Dapchi sai mahara suka kai hari makarantar suka sace yara 110 wadanda har yanzu ba'a san inda suke ba.

Gwamnan ya kara da bada misalin abun da ya faru a Bunu Yadi a shekarar 2014 inda mahara suka hallaka dalibai fiye da 50 a makarantar gwamnatin tarayya tare da yiwa makarantar kaca-kaca. Inji gwamnan, sai da aka janye sojoji daga garin kana 'yan Boko Haram suka kai hari makarantar. A cewar gwamnan haka ma lamarin ya faru a garin Dapchi. Sai da aka janye sojoji aka kai hari.

Sai dai rundunar sojojin ta ce a iyakar saninsu suna aikinsu ne yadda yakamata. Rundunar ta ce suna kakkabe 'yan Boko Haram daga dajin Sambisa baicin kwato garuruwa da dama. A sanarwar rundunar duk lokacin da suka kwato wani wuri sukan mikawa jami'an tsaro ne, wato, 'yan sanda, su kuma sojoji su ci gaba da yakinsu da 'yan ta'adda. Sojojin na ganin bai kamata gwamnan ya yi irin kalamun da ya yi ba.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Yobe Ya Ce Sakacin Sojoji Ne Ya Yi Sanadiyar Sace 'Yan Matan Dapchi - 4' 33"