Gwamnan Ohio ya janye daga neman takarar shugabancin Amurka

John Kasich yayinda yake bada sanarwar janyewarsa daga takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican

Gwamnan jihar Ohio John Kasich ya janye daga takarar neman Shugabancin Amurka jiya Laraba, ya bar abokin hamayyarsa Biloniyan nan mai harkar gidaje kuma tauraron Talbijin Donald Trump, wanda ake hasashen zai zama dan takarar Republican.

Kasich yace ba zai taba jin cewa wai ya tsorata ba ne, duk kuwa da cewa Trump din ya masa fintinkau a zaben fidda gwanin da ake yi. Dan takarar ya dan yi rauni a lokacin da yake jawabi yadda ya hadu da magoya bayansa a tarurrukan da aka yi.

Ya kira wannan da cewa ba karamin abu ba ne a gareshi da ya ga kamar almara na kaunar da aka nuna masa. To amma magoya bayansa sun dan damu da yadda ya janye daga takarar.

A baya Kasich da kyar ya samu wakilai 153. A jiharsa da yake wa gwamna a zaben fidda gwani daya kacal ya samu. A shekaran jiya ne dama Sanata Ted Cruz da ke biye da Trump ya ajiye tasa takarar.

Lokacin da aka faro wannan zaben fidda gwanin na ‘yan Republican suna da ‘yan takara guda 17 ne gaba daya a karkashin jam’iyyar. Kasich da Cruz sun yi iya kokarinsu su hana Trump samun yawan wakilai amma abun ya faskara.