Gwamnan Neja Ya Gargadi Kiristocin Jihar da Zasu Israila Su Bi Doka

Kiristocin Neja masu zuwa Israila aikin ibada

Alhaji Abubakar Sani Bello ya yiwa kiristocin jihar da zasu aikin ibada Israila da su bi dokokin kasar da zasu yayinda da yake sallamarsu kafin su tashi

Mutanen da zasu Israila daga jihar Nejan su dari da bakwai ne wadanda gwamnan jihar ya shaidawa suna wakiltar Najeriya ce gaba daya ba jihar Neja ba kawai saboda haka ya kirasu da su kiyaye halayensu.

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello

Akan masu tafiya da wata manufa daban walau ta makalewa a kasar ta Israila ko kuma su nufi wata kasa daban, yace idan har basu dawo ba zasu wahala domin babu wata kasa kamar Najeriya.

Shugaban tawagar maniyatan na jihar Dr El-Hakim Sama'ila ya bada tabbacin zasu sa idanu domin tabbatar da cewa ba'a karya dokokin Israila ba.

Tafiyar ta zo daidai lokacin da ake fara bukuwan kirsimati da na sabuwar shekara. Dr Sama'ila yace zasu yi anfani da zuwansu su yiwa kasar Najeriya addu'ar samun salama domin idan bashi kowa zai sha wuya.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Neja Ya Gargadi Kiristocin Jihar da Zasu Israila Su Bi Doka - 2' 56"