Gwamnan ya furta hakan ne a wajen taron shugabannin makiyaya da manoma da jami'an 'yansanda, da 'yansandan farin kaya da sarakunan gargajiya da bangarorin biyu jiya Laraba.
Gwamnan yace kada a zuba guba cikin ruwa ko ciyawa da nufin kashe dabbobi. Ya kuma kara da cewa idan aka bar arewacin Najeriya a duka kudancin kasar babu wata jiha da take da kyakyawar muamala tsakanin Hausawa da Yarbawa da Fulani kamar jihar Oyo.
Shi ma kwamishanan 'yansandan jihar Leye Oyebade cewa ya yi abun da suke yi shi ne su samarda zaman lafiya mai mahimmanci a jihar. Yace ba'a son duk abun da zai haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi kana ba'a son abun da ya faru a jihar Enugu ya faru a jihar Oyo.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello yace bayanin gwamnan nada mahimmanci. To saidai dangane da shirin gwamnatin na samar ma Fulani fili wanda zasu dinga biyan haraji a kai, Alhaji Yakubu yana da dan shakka akan hakan.Yace zasu koma wurin sarakunansu da dattawansu domin su bada shawara wadda zasu yi aiki da ita.
Mahalarta taron sun bayyana nasu ra'ayin.Wakili Isa Adamu yace sun yi murna da maganar gwamna Ajimobi. Yace gwamnan ya kawo shawarar zaman lafiya. Shi ma manomi Daramola Yomi yace gwamna ya nuna masu yadda zasu zauna da makiyaya Fulani.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5