Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya fadi cewa ba sa adawa da fulani makiyaya muddin masu neman halal dinsu ne, amma suna adawa da masu aikata laifuffuka kamar fyade, fashi da makami, garkuwa da mutane da dai sauransu, ba tare da la'akari da kabila, ko addini ba.
Gwamnan ya kuma ce dukkan masu haddasa fadan jinsi, za a kama su a hukunta su.
Da suke maida martani game da kalaman gwamnan, shugabannin Hausa/Fulani kamar Ibrahim Jijji, shugaban kungiyar Myetti Allah ta jihar Oyo, ya ce sun ji dadin abinda gwamnan ya fada. Ya kuma ce dama sun tabbata zai yi musu adalci, mussaman masu neman halal.
Jijji ya kuma ce su ma su na adawa da masu aikata manyan laifuffuka, don a cewarsa zaman lafiya suke nema, amma kuma su na fatan gwamnan zai neme su ya tattauna da su akan duk wani abu da za a yi da zai shafesu bisa ga tsarin doka a kuma yi binciken lamarin.
Shi ma Ado Suleiman sarkin Hausawan yankin, ya ce maganar da gwamnan ya yi magana ce ta gaskiya, ya kara da cewa bai dace a ce a kullum bafulatane ne kadai a ke kira barawo ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5