ZABEN2015: Mu'azu Akan Rikicinsa Da Mataimakinsa a Neja

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja.

A karon farko, gwamnan jihar Niger Muazu Aliyu Babangida yayi magana akan rikicin dake tsakaninsa da mataimakinsa Musa Ibeto

A karon farko gwamnan jihar Niger, arewa maso yammacin Nigeria, Muazu Aliyu Babangida, yayi magana akan rikicin dake tsakaninsa da mataimakinsa Alhaji Musa Ibeto.

Haka kuma gwamnan Aliyu ya yiwa wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari bayanin dalilin cire ofishin mataimakinsa daga gidan gwamnati da kuma rikon kwaryar da ya baiwa kakakin Majalisar wakilan jihar Niger, maimakon ya baiwa mataimakinsa.

Gwamnan Babangida yace gyara za'a yi, shi yasa aka cire ofishin. Akan batun rikon kwaryar da ya baiwa kakkakin Majalisar jihar, gwamna yace mataimakinsa ya aiko masa da wasika cewa zai yi tafiya. Shi yasa ya baiwa kakakin Majalisar rikon kwarya kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.

To amma kuma duk da wannan bayanin, jam'iyar APC ta masu hamaiya bata gamsu a cewar mai magana da yawun jam'iyar

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan jihar Niger yayi magana akan rikicinsa da mataimakinsa a karon farko 3.16