Gwamnan yana jawabi ne a lokacin da tawagar sarakunan ta kai masa gaisuwar sallah a gidan gwamnati.
Yace gaisuwar ita ce ta karshe da zasu kai masa a matsayinsa na gwamnan jihar. Sabo da haka yake neman gafarar sarakunan. Gwamnan yayi godiya da irin rikon da sarakunan suka yi masa. Yayin da ake tafiya tare dole an dan yi wasu kurakurai da batawa juna rai. Yace yana ganin sarakuna biyu ko uku ne bai batawa rai ba a cikinsu. Yace idann abun da ya batawa wani rai a cikin aikinsa sai a yafe masa.
Gwamnan da ake zaton zai nemi kujerar sanata a zabe mai zuwa yace a mako mai zuwa ne zai bayyana sunan wanda zai goyi bayansa domin ya gajeshi a matsayin gwamnan jihar daga cikin mutane bakwai gake neman mukamin idan Allah ya so hakan. Cikinsu kuwa har da mataimakin gwamnan Alhaji Ahmad Isa Ibeto da kuma shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Alhaji Umar Nasko.
Tun da farko dai shugaban majalisar sarakunan jihar Neja Etsu Nupe Alhaji Alhaji Yahaya Abubakar ya yaba da irin goyon bayan da gwamnan ke basu kana yace suna cigaba da yin iya kokarinsu wajen fadakar da jama'a mahimmancin zaman lafiya ga kasa. A halin yanzu suna fadakar da mutane game da mahimmancin yin tsafta domin magance cututtuka har da cutar ebola.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5