Yayinda yake zantawa da Muryar Amurka gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello yace an bude sabon kamfanin sarafa shinkafar ne a garin Bida a karkashin wani shirin hadin gwuiwa tsakanin gwamnatocin tarayyar Najeriya da jihar Neja da kasar Koriya.
Gwamnan yace sun bude kamfanin ne saboda yana cikin ayyukan da suka sa gaba zasu yi domin samun sarafa kayan anfanin noma da samar wa jama'a aikin yi.
Kowane awa daya kamfanin zai sarafa shinkafa tan daya da rabi wato cikin awa takwas zai sarafa tan 12 ke nan.
Kamar yadda gwamnan yayi bayani za'a dankawa wani kamfanin da zai dinga gudanar da harkokin sarafa shinkafa. Kamfanin zai dinga sayen shinkafa daga manoma ya sarafa kana ya sayar. Ba za'a bari ya shigo da shinkafa daga waje ba.
Kungiyoyin manoma sun yi maraba da zuwan kamfanin wanda suka ce zai taimaka wajen cigabansu. Alhaji Shehu Galadima shugaban hadaddiyar kungiyar manoma a jihar yace kamfanin zai fadada ayyukan manoma zai kuma kara masu arziki.
Alkalumma sun nuna Najeriya na bukatar shinkafa tan miliyan tara maimakon tan miliyan biyar da yanzu ake samu cikin gida.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
```````````````````````````````````````````````
````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````````