Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bayyana Gaban Kwamitin Bincike

Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana a gaban kwamitin bincike da majalisar jihar ta sa alkalin alkalan jihar ya kafa domin binciken gwamnan akan zargin da ake yi masa

Suleiman Dikko alkalin alkalan jihar Nasarawa shi ya nada kwamitin binciken biyo bayan umurnin majalisar dokokin jihar domin binciken zarge-zarge goma sha shida da aka yi masa.

Jiya gwamnan ya gabatar da kansa gaban kwamitin dake bincikarsa domin ya kare kansa daga zargin 'yan majalisar.

Bayan an tashi daga taron kwamitin wakiliyar Muryar Amurka ta zanta ta Abdulhamid Yakubu Kwara mai ba gwamnan shawara akan harkokin jama'a domin jin abubuwan da gwamnan ya gabatar a gaban kwamitin.

Gwamnan ya gayawa kwamitin abubuwa guda uku. Na farko yace ya zo ne saboda girmama kwamitin kuma a matsayinsa na mai bin doka, kuma wanda ya dauki Kur'ani yayi rantsuwa a kai cewa zai kare hakin kowane bil Adama.

Abu na biyu shi ne ya nunawa kwamitin cewa gaskiya ba'a yi masa adalci ba domin tun ranar 14 ga watan jiya da 'yan majalisa suka yi yunkurin tsigeshi har zuwa lokacin da ya bayyana gaban kwamitin ba'a bashi takardar zargin ba.

Abu na uku ya bayyana gaban kwamitin ne ya nuna masu da duniya gaba daya cewa a gwamnatinsa babu wani abu na nunafunci ko wani kunbiya-kunbiya dangane da karyar da aka yi masa domin ya kare sunansa da sunan gwamnatinsa ya kuma nunawa jama'ar jihar Nasarawa cewa shi mai rikon amana ne.

Bayan ya bayyana jiya gwamnan yace lauyoyinsa ne zasu cigaba da bayyana a gaban kwamitin din har sai ranar da suka gama shiri.

Yayin da gwamnan ya je gaban kwamitin, 'yan majalisar basu kasance wurin ba. Tun can baya majalisar tace ba zata amince da rahoton kwamitin din ba domin akwai ma'aikatan gwamnati da 'yan jama'iyyar gwamnan a ciki.

Shugaban kwamitin yace ya basu har zuwa yau idan ba'a samu an basu hannu da hannu ba to a manna a jikin bangon majalisar.

Ga rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bayyana Gaban Kwamitin Bincike - 3' 19"