Bayan fadan da ya faru a garin Debi cikin jihar Maradi mutane uku suka rasa rayukansu har da sarkin garin. Sai dai tuni wanda ya kashe sarkin ya mika kan sa ga hukuma
Gwamnan jihar Maradi Alhaji Zakari Umaru ya ziyarci garin kuma ya yi jawabi. Yace “ duk jama’ar Maradi suna yi maku ta’aziya”. Ya yi fatan Allah ya kwantar masu da hankali bisa abun da ya faru.
Sai dai gwamnan ya nuna damuwarsa yadda mutanen garin suka maida martini fiye da abun da aka yi masu. Yace bin doka shi ne abu na fi a’ala domin idan ba’a bin doka babu wanda zai rayu. Yana mai cewa su da suke shugabanci doka ta basu iko amma akwai yadda za su yi anfani da ikon da suke dashi. Idan an zalunci mutum cewa aka yi a kai kara wajen hukuma ba mutum ya aiwatar da nashi hukumcin ba, inji gwamnan. A cewarsa zasu bari doka tayi aikinta.
Ofishin ministan cikin gida na jamhuriyar Niger ya fitar da wata sanarwa inda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5