Da wakilin Muryar Amurka ya ziyarci gwamnan jihar Imo domin ya bayyana shirin yiwa 'yan asalin arewa rajistan samun katin izini zama cikin jihar ya samu wata amsa daban.
Gwamna Rochas Okorocha yace batun yiwa 'yan asalin arewa rajista abun ne dashi bai san kanshi ba. Yace batun ba gaskiya ba ne kuma hakan bai faru ba. Yace babu lokacin da gwamnati ta bada izinin a yiwa 'yan arewa rajista. Yace idan an tambayi 'yan arewan dake jihar ta Imo zasu tabbatar cewa ba'a yi hakan ba. Gwamnan yace yana ganin wata irin siyasa ce inda ake neman harzuka 'yan majalisar dattawa su dauki wani mataki akan jihar. Yace abun ya bashi mamaki.
A firar tasu gwamnan ya tabo tarihin alakarsa da arewacin Najeriya lamarin da yasa ba zai taba gyamar 'yan arewa ba. Yace akwai wani abu tsakaninsa da 'yan arewa tun ba yau ba. Yace akwai lokacin da aka kishi da iyayensa a jihar Imo. Sun bar jihar ne da yunwa suka nufi arewa. A arewa yace ya sayar da kwakwa da lemu da goro domin talauci. Sai ya gama talla da safe kafin ya je makaranta. A arewa yayi wannan abun inda aka karbeshi hannu biyu-biyu. Yace basu kishi ba. Yau kuma ace ya zama wani abu sai ya ki dan arewa. Yin hakan ba zai yiwu ba.
Gwamnan ya sake tabo wasu batutuwa da suka shafi siyasa musamman rashin hadin kan 'yan jam'iyyarsa ta APC. Yace rashin hadin kan 'yan jam'iyyarsa ka iya mayar da hannun agogo baya a kokarinsu na kwace mulki daga hannun PDP mai mulkin Najeriya a zaben 2015. Yace idan da PDP tana aiki yadda ya kamata da yau babu APC. Mutane sun gaji ne da yadda abubuwa ke tafiya. Damuwar APC yanzu shi ne hadin kai. Idan basu hada kai ba karbe gwamnati daga PDP ba zai yiwu ba. Idan ba hadin kai zasu sha wahala har da kasar.
'Yan arewa dake jihar sun bayyana irin takurar da suke samu. Sun ce duk inda suka wuce da doguwar riga sai a kirasu Boko Haram alhali kuwa su basu san Boko Haram ba.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.
Your browser doesn’t support HTML5