Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar bayan dawowarsa daga babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Yace babu wata kungiya ko kuma hukuma mai zaman kanta da ta basu wani tallafi na kudi domin tallafawa 'yan gudun hijira. Sai dai kungiyoyin da hukumomin kan baiwa 'yan gudun hijiran kayan tallafi da suka hada da abinci da magunguna da kayan karatu. Baicin irin wadan nan babu wasu kudade da wata kungiya ko hukuma ta taba jihar a matsayin tallafin taimakawa 'yan gudun hijira.
Yace tunda ya karbi mulki a shekarar 2011 zuwa yanzu gwamnatinsa ta karbi nera miliyan dari uku da arba'in da biyar ne kawai a matsayin taimako cikin shekaru biyar din da suka gabata.
Inji gwamnan, nera miliyan dari uku da arba'in da biyar basu isa su ciyar da 'yan gudun hijira ba koda na tsawon wata guda. Tsohuwar gwamnatin Jonathan ta basu nera miliyan dari biyu. A lokacin ne gwamnatin ta ba jihohin Adamawa da Yobe kowannensu nera miliyan dari da hamsin.
Gwamnan ya cigaba da cewa ko bayan rikicin Baga gwamnatin tarayya ta amince ta bada nera biliyan daya da miliyan daya na sake gina garin amma da suka nemi a basu kudin sai gwamnatin tarayya ta hana.
To saidai akwai wasu jihohi da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka taimaka da kudade. Idan aka hada kudin da suka basu da na gwamnatin tarayya shi ne zai bada jimillar nera miliyan dari uku da arba'in da biyar din.
Jihar ta samu tallafi da dama daga wasu kasashen ketare amma basu bada kudi kai tsaye ba ga gwamnati. Sun kawo tallafi na kayan abinci da magunguna da dai wasunsu.
Gwamna Shettima yace bai san yadda batun cewa gwamnatin jihar ta karbi biliyoyin nera ke fitowa ba. Yace tun a ranar 18 ga watan Fabrairu ne hukumar bada agajin gaggawa ko NEMA ta yanke samar da abinci ga gwamnatin jihar Borno.
Gwamnan ya kuma amsa tambaya akan karkata abincin 'yan gudun hijira da aka ce wasu hukumomi na yi a jihar. Yace ya umurci 'yansanda har da na fararen kaya da su binciki faifan bidiyon dake yawo yana nuna irin abun da hukumomin ke yi. Bidiyon ya nuna ana canza buhun abinci ana kuma shiga dasu kasuwa domin sayarwa. Bayan bincike gwamnan yace ba zasu kyale duk wanda aka sameshi da hannu a badakalar ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5