Gwamnan jahar Bauchi, Abdulkadir Bala Muhammed Kauran Bauchi, ya kuduri aniyar ganin an kawo daidaito a rikicin da ya faru tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
Kauran Bauchin ya yi wannan furucin ne a fadar gwamnatin jahar Bauchi, a lokacin da tawagar da sarkin Kano ya tura bisa jagorancin Makaman Kano, Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, domin Kai ziyarar taya shi murnar nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Bauchi.
A jawabinsa, gwamnan jahar Bauchi Abdulkadir Bala Muhammed Kauran Bauchi, ya bayyana takaicinsa dangane da yanayin da masarautar Kano ta samu kanta ciki, ya ce Kano ita ce abin misali ga dukkan bahaushe da kuma arewacin Najeriya, sabili da haka wargaza ta babbar gobara ce da ya kamata a kasheta.
Tunda farko kuwa, jagoran tawagar, Makaman Kano Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, ya fayyace wa gwamnan makasudin kawo ziyarar da mai martaba Sarkin Kano Muhammadau Sunusi na biyu ya umurce su da su kawo.
A gefe guda kuma, gwamnan jihar Bauchin ya kai mubaya’a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin fayyace masa yadda abubuwa ke gudana a jahar Bauchi a siyasance.
Ga Rahoton Abdulwahab Muhammed Cikin Sauti.
Your browser doesn’t support HTML5