Gwamnan Imo Ya Nuna Sha'awar Shiga Takarar Shugaban Kasa a Inuwar APC

APC

Da alamu jam'yyar APC wadda kawo yanzu duk 'yan takararta dake neman shugabancin Najeriya daga arewacin kasar suka fito, zata samu akalla daya daga kudancin kasar.

Wannan zai faru ne biyo bayan nuna sha'awar da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yayi.

Gwamna Okorocha ya nuna sha'awar ne a taron matasan arewacin Najeriya da aka yi a Kaduna. A wurin taron matasan sun nemi ya yiwa Allah ya fito takarar neman kujerar shugaban kasar Najeria a zaben 2015.

Yayin da yake mayar da martani gwamna Okorocha ya nunawa matasan irn matsalolin da suka addabi kasar. Yace a kasar akwai matsala. Ana wahala. Yace akwai abubuwa biyu dake damun kasar. Akwai talauci. Na biyu akwai yaudara. Wadannan sun damu kasar yayin da shugabannin kasar sai kabilanci da banbancin addini suke nunawa.

Shugabanni basu shirya yadda yara zasu samu karatu ba. Basu kuma tanadi ayyukan da matasa zasu iya yi ba. Basu kula da samar da isasshen abinci ba.

Yace ya gayawa Allah idan har zamansa shugaban kasa ba zai kawo zaman lafiya ba, ba zai bada ilimi kyauta ba daga firamare zuwa jami'a, kuma ba zai kawo karshen kashe-kashe ba to shi baya so.

Jawaban na Gwamna Okorocho sun nuna zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC. Yace an dade ana yaudarar 'yan Najeriya saboda an sha yi masu alkawura kuma basu gani a kasa ba. An yi alkawarin bada wuta, ruwa, hanyoyi da asibitoci duk ba ko daya da aka gani.

Ana son shugaba da zai yiwa dan talaka aiki ba ya sa batun addininsa gaba ba ko kabilarsa. Tambaya a nan ita ce idan kana son shugabanci menen zaka yiwa talaka.

Idan gwamna Okorocha ya zama shugaba yace makaranta zata zama kyauta, wato babu biyan kudin ilimi daga firamare har zuwa jami'a kamar yadda yake yi yanzu a jihar Imo.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Imo Ya Nuna Sha'awar Shiga Takarar Shugaban Kasa a Inuwar APC - 4' 10"