Gwamnan jihar Ekiti yace a halin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari yake ciki babu abun da zai ce sai dai ya yi masa addu'a Allah ya bashi lafiya.
Da aka ce masa a can baya an sanshi da sukar shugaba Buhari, gwamna Fayose yace ba wai yana fada da shugaba Buhari ba ne, a'a yana tunanen 'yan Najeriya ne da suka zabeshi ne. Allah ya bashi lafiya domin su sami abun da suke so, wato, ya yi masu aikin da suka zabeshi yayi. Yace shi yana kan gaskiya ne.
Akan ko yanzu ya canza ra'ayinsa ne sai gwamnan yace laifi ne ya yiwa wanda bashi da lafiya addu'a. Yace shi bai canza matsayinsa ba.Yace shi yana nan akan gaskiya.
Dangane da abun da yake son 'yan Najeriya su yiwa shugaba Buhari sai gwamnan yace su ma su yi masa addu'a domin ya warke da wuri yayi masu ayyukan da suka zabeshi.
Batun kiraye kirayen da wasu kungiyoyi su keyi cewa shugaban ya sauka daga karagar mulki, sai yace shi baya magana da kungiyoyi kamar su NGO. Fatansa shi ne Allah ya bashi lafiya domin ya samu ya cika akwuran da yayiwa 'yan Najeriya.
To saidai masu kula da lamuran yau da kullum suna ganin gwamna Fayose ya canza matsayinsa ne na sukar lamuran shugaba Buhari.
Your browser doesn’t support HTML5