Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da kwamitin ayyuka na musamman a karkashin shugabancin Sanata Abdulaziz Nyako ya ziyarceshi a fadarsa a Maiduguri.
Gwamnan ya shaidawa 'yan kwamitin ya fahimci cewa kungiyoyi masu zaman kansu suna tattara kudade ne da sunan 'yan gudun hijira amma a kasari basa tallafawa 'yan gudun hijiran yadda ya kamata. Gwamnan yace babu abun da su keyi illa sayen motoci masu tsada tare da gina manyan gidaje a yankunan GRA.
Alhaji Kashim Shettima yace ba zasu lamunta da irin halin kungiyoyin ba. Yace kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun ce sun kashe dalar Amurka miliyan 334 a jihar Borno to amma ba'a gani a kasa ba. Kungiyoyin sun kashe wajen nera miliyan hamsin wajen sayo motocin da harsashi baya ratsawa cikinsu domin anfaninsu.
Acewar gwamnan da zara ya hana kungiyoyin shiga sansanin kungiyoyin kare hakkin bil Adama zasu soma cewa ana tauye hakkin mutane. Yace ko menene zasu yi nasu ikon a gwamnatance su dakile zaluncin da ake yi, ana karbo taimako da sunan 'yan gudun hijira amma ana dannewa.
Yawancin sansanin basa samun ruwan sha ko na wanka kamar yadda Muryar Amurka ta gano. Yan sansanin ne suke karo karo su hada kudi su sayi mai domin tada injin dake jawo masu ruwa. Gwamnati bata taimaka masu haka kuma kungiyoyin agaji basu damu dasu ba.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5