Gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar yace kudin nan na Paris Club hakkin jihohi ne kuma suna ma neman kari.
Gwamnan ya yi magana ne bayan taron Majalisar Tattalin Arziki ta Najeriya. Ya ce ba daidai ba ne a dinga zargin gwamnoni da kasa biyan albashi don da yawansu suna da hujja. Ya yi misali da jihar Benue da ta gaji bashin albashin da ya wuce hankali.
A cewar gwamnan na Buachi, bashi ne da gwamnatin tarayya ta ciwowa jihohi da kananan hukumomi tun a lokacin gwamnatin Obasanjo wacce ta dauki kudin aka biya Paris Club ba tare da yin la’akari da cewa na jihohi da kananan hukumomi bane. Gwamnan yace ba wai zuwa suke yi da kokon bara ba.
Gwamnan Bauchin yace shi kam yana biyan ma’aikatansa a kan kari.
Shi ma gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya musanta rade-radin cewa sojoji na gudanar da allurar rigakafin kyandar biri da ake zargin sojojin da yadawa da gangan.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5