Gwamnan Adamawa Ya Ziyarci Hamma da Wani Likita Ya Cire Kodojinsa

Gwamnan Adamawa Jibrilla Bindo yayinda ya ya ziyarci Isa Hama a asibiti

Watan jiya ne wani likita a Yola ya cire kodoji biyu na Isa Hamma saboda wai yana tunani wani tsiro ne na cuta a cikinsa.

Gwmnan na Adamawa ya ziyarci shi Isa Hamma ne a asibitin gwmnatin tarayya dake Yola, ko FMC a takaice, inda wannan mutumin da wani likita ya cire masa kodoji, yake kwance yau fiye da wata daya ke nan.

Isa Hamma yace shi bai san abun da ya faru ba sai da ya shiga wani mugun halli har suka je Gombe amma bai samu nasara ba. Isa ya nemi taimakon gwamnati da jama'a.

Labarin abun da ya faru da Isa Hamma ya tada hankalin mutane da dama har ma lamarin ya harzuka wani matashi daga jihar Taraba, Muhammad Sani. Shi wannan matashi yayi tattaki zuwa Yola inda ya kuduri anniyar bada kodarsa daya domin taimakawa Isa Hamma.

Malam Adamu Dodo jami'in hulda da jama'a na asibitin gwamnatin tarayya da ake kira FMC a takaice, ya bayyana taimakon da gwamnan Adamawa ya bayar.

Gwamna Bindo ya bada mota da taimakon nera miliyan biyar na tafiya da shi Isa Hamma da Muhammad Sani zuwa Kano inda za'a cire koda daya ta Muhammad a dasawa Isa Hamma. Idan Isa ya dace cikinsa ya karbi kodar to ya ci sa'a.

Shi likitan da ya aikata wanna danyan aikin yana hannun 'yansanda kuma za'a gurfanar dashi gaban shari'a.

Masana aikin likita sun yi tsokaci akan wannan danyen aikin. Muhammad Kabir Inuwa wani likita a Jalingo yace akwai abun dubawa. Yace abun da likitan yayi ganganci ne ko kuma bai je makarantar koyon aikin likita ba.

Ga rahoton Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan AdamawaYa Ziyarci Wanda Wani Likita Ya Cire Kodojinsa - 4' 07"