Gwamnan Adamawa Ya Musanta Zargi n Akwai Hannunsa Kwangilar Sayen Makamai

Jihar Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa Sanata Bindo Jibrilla ya karya zargin cewa akwai hannunsa a badakalar kwangilar sayen makamai da yanzu ta kaiga kama gwamnoni da manyan jami'an gwamnati.

Wasu kafofin yada labarai suka ruwaito cewa akwai hannun gwamnan a badakalar.

Ana zargin gwamnan ya karbi nera biliyan goma sha tara da sunan kwamitin tsaro yayinda yake majalisar dokokin kasar. Sanata Bindo wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin tsaro na majalisar yace shi ko kwandala bai karba ba daga ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki.

Gwamnan ya yi magana ne ta bakin kwamishanan yada labarai Ahmed Sajo yace ana neman bata masa sunan ne a badakalar. Mutane na son kawo rudani ne ko su ci masa mutunci domin cimma muradun mkansu.

Batun cuwa-cuwar sayen makamai ta riga ta jefa wasu kusoshin gwamnatin Jonathan da ta shude cikin rigima da yanzu suka fada hannun ECFF hukumar dake yaki da almundahana da cuwa-cuwa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Adamawa Ya Musanta Zargin Akwai Hannunsa a Kwangilar Sayen Makamai - 3' 20"