Wasu shugabanin yan kabilar Igbo ke nan yayin wani taron gaggawa da gwamnatin jihar Adamawa ta kira tare da jami’an tsaro na sanin matakan da suka kamata don kare rayukansu da kuma dukiya,biyo bayan tashe tashen hankulan da suka auku a kudu maso gabashin Najeriya da kuma wasu jihohin arewa,dake da nasaba da yan fafutukar kafa kasar Biafra.
Hukumomin tsaro dai a jihar Adamawan sun baiwa yan kabilar Igbon tabbacin kare rayukansu da ma dukiya,yayinda su kuwa ke yin tir da Allah wadai da abubuwan dake faruwa a yankin nasu na kudu maso gabashin Najeriyan.
Chief Sunday Onyebuchi na cikin shugabanin matasan kabilar Igbo a Najeriya yace sun amince da tabbacin gwamnatin jihar Adamawa ta kare rayukansu.
Bayan dai wannan taron gaggawan,Ahmad Sajo dake zama kwamishinan yada labaran jihar yayiwa manema labarai karin haske game da matakin da aka dauka yanzu inda yace tuni aka baza jami’an tsaro tare da yin kira ga yan kabilar Igbon da su kwantar da hankulansu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5