Gwamna Zulum Ya Umurci Biyan Ma'aikatan Jihar Borno Albashinsu

Dr. Babagana Umar Zulum

Gwamna jihar Borno Babagana Umar Zulum, ya bada umurnin biyan dukkannin ma’aikatan jihar da basu samu albashin su ba sakamakon wani aikin tantancewa da gwamnatin jihar Borno ta soma tun shekaru hudu da suka gabata domin tantace ma’aikata da 'yan fashon jihar.Wanda hakan ya haifar da rashin samun albashin wasu ma’aikata tare da wasu yan fanshon fanshon.

A baya baya ne kungiyar tsofofin yan fashon suka gudanar da zanga zangar rashin samun hakkokin su, A halin yanzu gwamna Zulum, ya dakatar da wannan tantacenwar domin a biya ma’aikatan albashin su inda yanzu haka akwai mutane kimanin 296 da ba’a biya su albashinsu ba duk da cewa an kammala aikin tantacen su.

Don haka ne, Gwamna Babagana Umar Zulum, ya umarci jihar da ta biya albashi da gaggawa. Ya kara da cewa, duk wani ma’aikacin da aka kama da laifin almundahana za’a hukunta shi domin kuwa ana samun ma’aikata da suke ansar albashi fiya da daya.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Bi'u

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Zulum Ya Umurci Biyan Ma'aikatan Jihar Borno Albashinsu