Gwamna Rauf Aregbesola Ya kai Ziyarar Ta'aziya Ile Ife

Rauf Aregbesola

A sakamakon rikicin Ile Ife, dake cikin jihar Osun, Gwamnan jihar Abdulrauf Aregbesola, ya kaiwa jama’ar Ile Ife, ta’aziya.

Muhammad Bashir, mai baiwa gwamna shawara dangane da abinda ya shafi ‘yanarewa dake jihar Osun, ne ya furta haka ga wakilin muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal.

Gwamnan ya jajantawa al’umar da kuma tabbatar masu da Karin tsaron da alkawarin cewa irin haka bazai saka faruwa ba, yana mai cewa kowane dan arewa, yana da ‘yancin daidai da kowa a jihar Osun, kamar yadda shara’a ta tanada.

A kuma kama wasu daga cikin wadanda suka hadasa wannan fitinar gwamnatin jihar ta sha alwashin cewa zata tabbatar cewa an gurfanar dasu gaban kotu da tabbatar da cewa an yanke masu hukunci daidai laifin da suka aikata.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Rauf Aregbesola Ya Kai Ziyarar Ta'aziya Ile Ife - 2'56"