Gwagwarmayar Saye Da Musayar Zaratan 'Yan Wasa Ta Kunno Kai

Thomas Lemar

A kokarin da kungiyoyin kwallon kafa na duniya ke yi na ganin sun kawo wasu ‘yan wasa kungiyarsu, wajan saye ko neman aro wanda za'a bude a watan janairu na shekarar 2018.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta sa kudi fam miliyan £80, wajen ganin ta dauko dan wasan gaba na Monaco, Thomas Lemar mai shekaru 22 da haihuwa wanda Liverpool da Arsenal, suke batun sayen sa a karshen kakar wasan bana.

Mai horas da kungiyar Westham, David Moyes, na shirin sayen jack Wilshere, daga kungiyarsa ta Arsenal a watan Janairu.

Mai tsaron baya na kungiyar Juventus, Alex Sandros, wanda Manchester United, take nema ya shaida wa kulob dinsa cewar yana da shi'awar barinsu amman yafi bukatar komawa kungiyar Chelsea, a watan Janairu mai zuwa da zarar an bude cinikaiya.

Antonio Greizman, ya bayayyana shi'awar sa ta barin kungiyar ta Atletico Madrid, da niyyar Komawa Barcelona, a karshen kakar wasan bana.

Arsenal, ta amince zata biya fam miliyan £35.3 kan sayen dan wasan Sevilla Steven N'zonzi, a watan janairu da zarar an bude hada-hadar saye da sayarwa.

Barcelona, tana dab da kammala cinikin dan wasan baya na kasar Colombia, mai taka leda a Palmeiras mai suna Yerri Mina, 23 don ya maye gurbin Javier Mascherano, dan shekaru 33 a duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwagwarmayar Saye Da Musayar Zaratan 'Yan Wasa Ta Kunno Kai