Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya damu da rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar Guinea Bissau inda shugaban kasar ya kori firayim minista daga mukaminsa ya kuma nada wani.
Shugaban kasar Jose Mario Vaz ya kori Firayim Minisata Domingos Simoes Pereira tare da ministocinsa daga mukamansu.
Saboda nuna dangantaka dake akwai tsakanin shugabannin kasashen Afirka Shugaba Muhammad Buhari ya tura tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo zuwa kasar Guineaa Bissau a matsayin manzo na musamman da nufin ya kawo daidaito tsakanin shugaba Mario Vaz da firayim ministansa Simoes Pereira domin tabbatar da zaman lafiyar kasar.
Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya fara aikin da shugaba Buhari ya bashi tare da tutubar shugaban kungiyar ECOWAS wanda kuma shi ne shugaban kasar Senegal Macky Sall a babban birnin kasar Dakar jiya.
To saidai abun takaici shi ne yayin da Olusegun Obasanjo yake tattaunawa da shugaban Senegal a Dakar jiya shugaban Guinea Bissau Mario Vaz ya sha gaban kansa ya nada Mr. Baciro Dja a matsayin sabon Firayim Ministan kasar.
Duk da haka shugaba Buhari ya nemi a kai zuciya nesa tare da kira ga shugaban kasai Guinea Bissau ya yi takatsantsan ya kiyaye doka da oda saboda kokarin da ake yi na shawo kan lamarin.
Musamman shugaban Najeriya ya kira shugabannin kasar da suka hada da na siyasa da sojojin kasar da su kiyaye da kundun tsarin mulkin kasar, su kare lafiyar jama'arsu su kuma kiyaye daukan duk wani mataki da ka yiwa dimokradiyar kasar barazana wadda aka soma ginawa kwana kwanan nan.