Sannan tayi sanadiyyar daukewar wutar lantarkin fiye da gidaje Miliyan 1, bayan ta hallaka akalla mutane 6 a birnin Taiwan. Ba wani rahoton wadanda suka jikkata akan doron kasa ko kuma asarar dukiya.
Ta kuma durkusar da hada-hadar birnin Putiyan mai dauke da yawan jama’ar da suka kai Dubu 450. Rahotannin kasar Sin sun ce, an sami yin gaggawar kwashe mazauna wajen kamar guda Dubu 158 don gujewa hatsarin abin.
Fiye da jiragen fasinja zuwa kasashen duniya da kuma cikin gida guda 300 ne suka kasa tashi don gudun faruwar hatsari. Ma’aikatar yada labaran Taiwan tace, a cikin wadanda suka mutu har da wata mata da danta mai kimanin shekaru 8 a duniya.
Wasu ‘yan tagwaye ma, sun bace tare da kuma kimanin mutane guda 60 da suka halaka. Wani faifan bidiyo a talabijin ya nuna yadda mutane da yawa ke tsatstsaye tsamo-tsamo ba matsuni.