Firai ministan kasar Carlos Do Rosario ya ce an samu mutuwar mutane biyar a wannan guguwar Kenneth. Kafin guguwar ta karaso Mozambique, sai da Kenneth ta yi barna a kasar Comoros ta kuma kashe mutane uku.
Hukumar kai agaji a lokacin bala’I ta kasar Mozambique ta ce guguwar Kenneth ta lalata sama da gidaje dubu uku kana ta fitar da sama da mutane dubu 18 daga gidajensu.
Gwamnatin kasar ta ce guguwar ta fi lalata gidaje a tsibirin Ibo na Mozambique, inda gidajen mutane dubu shida suka lalace.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya su tallafawa yankunan da guguwar ta shafa da taimako na gajere da matsakaici da ma na dogon lokaci.
A jiya Lahadi MDD ta bada kayan taimako na dala miliyan 13 da suka hada da abinci da wurin bacii da magunguna da ruwa da kayan tsaftace jiki zuwa mutanen da guguwar Kenneth ta shafa a Comoros da Mozambique.