'Yan jarida na bada gagarumin gudumawa wajen fadakarwa da illmantarwa akan batutuwan da suka shafi rayuwar jama'a.
A yayinda lokacin yin zabubbuka ke karatowa a Nigeria, wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji ta zanta da wasu 'yan jarida a jihar Plato akan irin gudumawar da suke bayarwa wajen ganin an gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba
Mr. Agabus dan jarida ne wanda yake aiki da Africa Examiner On Line. Yace suna kokarin fadakar da jama'a akan yadda ya kamata a gudanar da zabe bisa dokokin gwamnati ko kuma dokokin hukumar zabe mai zaman kanta. Haka kuma yace suna kokarin fadakar da jama'a dukkan abubuwan da hukumomi suka fada wadanda suka danganci zabe.
Shi kuma Mohammed Tanko Shitu, wakilin jaridar Blue Print ne dake birnin Jos. Yace musamman a wannan lokaci, 'yan jarida suna iya kokarinsu, kawai akan rahotani da suka danganci riki ko tashin hankali ba. Yace su kan yi dukkan abubuwan da suka san zai jawo hankalin mutane domin yin abubuwa cikin lumana.
Your browser doesn’t support HTML5