Dan wasan tsakiya dan kasar Switzerland ya ce ba zai sake barin duk wata dama da ya samu ba na jagorantar kungiyar ta Gunners ba, biyo bayan kubuta da kyar da kungiyar ta yi.
Granit Xhaka ya bayyana cewa kadan ya rage mishi ya bar kungiyar Arsenal a watan Janairu da ya gabata, yayin da kuma ya ce zai sake samun damar sake zama kaftin din Arsenal a nan gaba.
Tsohon kocin kungiyar Unai Emery shi ne ya nada Xhaka a matsayin sabon kaftindin dindindin na Arsenal, sakamakon ficewar Laurent Koscielny, a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa lokacin da ya nemi 'yan wasan su zabi wanda su ke so.
Dan kwallon Switzerland din ya dauki tsawon watanni a matsayin kaftindin kungiyar, amma bayan wani lamarin da ya faru tsakanin magoya bayan kungiyar yayin wasan da suka tashi 2-2 da Crystal Palace a filin wasa na Emirates a ranar 27 ga Oktoba bara.
Xhaka ya fice cikin fushi daga filin wasan bayan da 'yan kallo su ka yi masa ihu, shi kuma ya mayar musu da zagi.