GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Waiwaya Maganin Mantuwa: Kashi Na UKu, Disamba 20, 2018,

Grace Alheri Abdu

Yau ma shirin Domin Iyali yana waiwaya maganin mantuwa. A farkon wannan shekarar aka gayyaci mai martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi na biyu a Jamhuriyar Nijar, domin neman hanyar shawo kan kuntatawa mata inda a jawabinsa ya tabo batutuwa da dama da suka shafi aure da zaman gida da kuma koyarwar addinin Musulinci dangane da sunar aure.

Bayan nan Shirin ya kuma gayyaci masu ruwa da tsaki a Jamhuriyar Nijar domin bibiya kan wannan matsala.

Har wa yau, shirin ya nemi hanyar shawo kan gallazawa abokan zaman aure.

Your browser doesn’t support HTML5

Waiwaya Maganin Mantuwa-PT3

Kadan ke nan dake cikin batutuwa da muka tabo a shirin Domin Iyali a wannan shekara ta dubu biyu da goma sha takwas dake karewa. Za a iya neman dukan shirye shiryen da muka gabatar a shirin a wannan shafin na internet.