Idan kuna biye damu makon jiya muka gabatar da muryar Leah Sharibu da kungiyar Boko Haram ta fitar karon farko tunda saceta sama da watanni shida da suka shige, muryar da iyayenta Rebecca da Naniel Sharibu suka tabatar da cewa muryarta ce, suka kuma ce tunda aka saceta har zuwa lokacin da muka yi hira da su babu hukumomin da suka taba tuntubarsu dangane da lamarin.
Shirin Domin Iyali ya zanta da Barista Emmanuel Ogegbe wani lauya mai zaman kansa a nan Amurka kuma dan fafatukar kare hakkin bil’adama, da kuma Dr Kole Shatimma shugaban cibiyar bunkasa damokaradiya da ci gaba ta Najeriya, dangane da jin muryar Leah bayan sama da watanni shida da saceta. a hirarmu da shi da jin bullar wannan faifai. Dukansu sun bayyana bukatar gwamnatin tarayya ta kara himmatuwa wajen maida Leah ga danginta.
Sai dai duk yunkurin da muka yi domin jin ta bakin gwamnatin Najeriya ya cimma tura.
Saurari cikakken shirin
Your browser doesn’t support HTML5