WASHINGTON, DC —
Wata kotun soja ta musamman da ta zauna a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, ta ragewa wani babban jami’in soji girma ta kuma kore shi daga aiki bayan samunshi da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekaru goma sha hudu fyade a Maiduguri inda aka tura shi aikin kare rayukan al’umma da kuma murkushe kungiyar Boko Haram dake tada kayar baya.
Bisa ga bayanin, yarinyar ta tafi bayan gari neman itacen wuta ne tare da wadansu yara da suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijiran da ake kira Bakassi Camp, lokacin da babban hafsan sojan ya sa suka kwakkwanta ya ware yarinja ya shigar da ita jeji inda ya yi mata fyade.
Saurari cikakken bayanin a wannan shirin.
Your browser doesn’t support HTML5