Masu kula da lamura kan harkokin siyasar Najeriya sun bayyana cewa, tilas ne jam'iyun siyasa su sake lale, yayinda kuma a nata bangaren ya kamata gwamnati ta kafa dokar da zata tabbatar da cika alkawarin ba mata damar tsayawa takara su kuma shiga a dama da su a gwamnati kamar yadda Najeriya ta amince tare da sa hannu a kudurin da ya bukaci a ba mata kashi talatin da biyar cikin dari na mukaman siyasa.
Domin bibiya kan wannan batun, shirin Domin Iyali ya gayyaci Barrister Badiha Abdullahi Mu'azu 'yar gwaggwarmayar kare hakin bil'adama, da Hajiya Hauwa El-Yakub mai neman tsayawa takarar majalisar dattijai karkashin tutar jam'iyar NPM domin wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, da kuma, Kwamred Sa'idu Kabiru Dakata darektan cibiyar wayar da kan al'umma game da shugabanci na gari.
Saurari bayanansu a wannan tattaunawa da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:
Your browser doesn’t support HTML5