GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Nazarin Wa'adin Farko Na Mulkin Buhari-Mayu, 30, 2019

Grace Alheri Abdu

Jiya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauki rantsuwa da a hukumance ya fara wa’adin mulki na biyu, bayan yakin neman zabe da burin dorawa a kan aikin da ya yi cikin shekaru hudu da suka shige, wadanda ake samun ra’ayoyi masu karo da juna kan nasarori da gwamnatin ta cimma.

Shirin Domin Iyali ya nemi jin ta bakin mata da ake yiwa kirari da iyayen tafiya kan wa’adin farko na shugaba Buhari. A bayaninta, Barrista Sa’ida Sa’ad wata lauya kuma ‘yar gwaggwarmaya ta bayyana nasarori da gwamnatin ta cimma da suka hada da fannin tattalin arziki da noma da samar da aikin yi ga matasa. .

A nata bayanin, Hajiya Mariya Ibrahim Baba wadda ta taba tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa karkashin tutar jam’iyar People’s Progressive Alliance PPA tace duk da yake gwamnatin Buhari ta sami nasarori a fannoni da dama, tana da rauni a wurare da dama.

Saurari cikakken shirin.

Your browser doesn’t support HTML5

Nazarin wa'adin farko na mulkin Buhari-10:20"