GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Afrilu 19, 2018: Cika Shekaru Hudu Da Sace 'Yammatan Chibok, Kashi Na Daya

Grace Alheri Abdu

Yau Alhamis 19 ga watan Afrilu aka cika kwanaki dubu daya, da dari hudu, da arba'in da takwas, da sace yanmatan Chibok 276. Da kawo yanzu, gwamnati ta sami nasarar ceto 107, 57 kuma suka dawo gida da kansu. Yayinda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da rike yammata dari da goma sha biyu, da kuma Leah Sharibu daliba daya tilo da kungiyar taki saki, domin taki ta Musulunta, daga cikin dalibai dari da goma da ta sace ranar goma sha tara ga watan Fabrairu a garin Dapchi.

A cikin shekaru hudu nan Kungiyoyi daban daban suyin yi ta yekuwar neman a sako, ko kuma Gwamnati ta kwato sauran ‘yammatan da har yanzu suke hannun wadanda suka sace su.

A cikin shirye shiryen fafatukar da kungiyar BBOG ke yi, Bana an yi jawabai a Babban birnin Tarraiyya Abuja, inda aka sake kira tareda matsa lamba, da kira ga Gwamnati ta sake salon yakin kwato 'yan matan.

Wakiliyarmu Medina Dauda, tayi hira da Hajiya Naja’atu Mohammed daya daga cikin wadanda suka yi jawabai a wurin taron.

Your browser doesn’t support HTML5

Cika Shekaru Hudu Da Sace Yammatan Chibok-10:05"