GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Garkuwa Da Mata A Jihar Katsina, Satumba,12, 2019

Alheri Grace Abdu

Al’ummar garin Shinfida na jihar Katsina sun shiga halin ni'yasu sakamakon garkuwa da iyalansu da 'yan bindiga suka yi bayanda suka yiwa wani ayarin motoci dake kan hanyar cin kasuwa kwantan bauna suka sha karfin jami’an tsaro daga nan suka tasa keyar matan da aka bari a mota. Shirin Domin iyali ya zanta da wadansu da wannan lamarin ya shafa wadanda kuma zamu saya sunayensu bisa dalilan tsaro.

Saurari cikakken bayanan magidantan da aka yi garkuwa da iyalansu da kuma hirar da shirin ya yi da daya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su.

Your browser doesn’t support HTML5

garkuwa da mata a shinfita Pt1-10:30"