GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Garkuwa Da Mata A Jihar Katsina, Kashi Na Biyu-Satumba,19, 2019

Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye damu, makon da ya gabata shirin ya yi hira da wadansu a jihar Katsina da ake fama da haren haren 'yan bindiga. 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mata da kananan yara a garuruwa da dama da ya hada da garin Shinfida. A cikin hirarmu da daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da iyalinsa wanda muka saya sunansa sabili da dalilan tsaro ya bayyana takaicin gaza iya shawo kan maharan da yace suna da makamai da suka fi na jami'an tsaro da aka tura yankin.

A cikin hirarsu da Shirin Domin Iyali, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakin sulhun ne domin ba maharan damar sake shawara su rungumi dabi'ar kwarai amma idan suka ki za a shiga yaki da su sai an ga bayansu baki daya.

Saurari cikakken shirin domin jin abinda al'ummar shinkafi ke cewa game da wannan lamarin da kuma matakan da gwamnatin jihar Katsina ta dauka kawo yanzu.

Your browser doesn’t support HTML5

Garkuwa da mata a jihar Katsina-10:30"