GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Bibiya Kan Batun Ba Mata Kashi 35 Cikin Dari Na Mukaman Dori-Kashi Na Daya-Yuni, 06, 2019

Grace Alheri Abdu

Bayan rantsar da shugabannin siyasa a matakin tarayya da kuma jihohi a Najeriya, inda hankali ya karkataq yanzu shine raba mukamai da suke galibi na dorawa ba zabe ba, abinda ya sa mata yin gangami na neman a cika alkawarin basu kashi talatin da biyar cikin dari na guraban.

Bisa ga dukan alamu kuma hakar na iya cimma ruwa ganin kamun ludayin wadansu gwamnoni kawo yanzu.

Shirin domin iyali ya gayyato masu ruwa da tsaki Hajiya Hauwa El-yakub wadda ta tsaya takarar wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattijan tarrayar Najeriya sai dai hakarta bata cimma ruwa ba, da kuma barrista A'isha Ali Tijjani yar gwaggarmayar kare hakkokin bil'adama musamman mata domin bibiya kan batun.

Saurari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Neman ba mata guraban siyasa a Najeriya PT1-10:30"