Gowon Ya Bukaci ECOWAS Ta Dage Takunkunmin Da Ta Kakaba Wa Mali, B’Faso, Guinea Da Nijar

Your browser doesn’t support HTML5

Tsohon shugaban Najeriya kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin nahiyar Afrika, Janar Yakubu Gowon, ya bukaci ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakabawa kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.