Google Zata Taimakawa Masu Kirkirar Fasahar Manhajar Wayoyin Hannu

Google

Google ya amince zai sayi wani sashen kamfanin Twitter, da yake taimakawa masu kirkirar fasahar manhajar wayoyin hannu wato Application, wanda shine kokarin da Twitter ya yi na baya bayan nan don bunkasa kasuwancinsa.

Kamfanin Twitter ya kaddamar da wannan sashen ne da ya kira Fabric a shekara ta 2014, wanda yanzu haka sama da makirkira manhaja 580,000 ke amfani da wannan fahasa.

Baki daya ma’aikatan sashen Fabric zasu koma aiki da Google, sai dai har yanzu Twitter bai sanar da yawan ma’aikatan ba, kuma bai fitar da wani bayani da ke nuna adadin kudin da zai sayar da wannan sashen Fabric ba.

Fabric dai wani bangare ne a kokarin da Twitter yayi na inganta kafe sakonnin Twitter da mutane ke yi kai tsaye, inda ya kirkiri hanya da za ta saukakawa masu kirkirar manhaja a lokacin da fasahar wayoyin hannu ke mamaye duniya.

Idan har Google ya sayi Faric, zai zamanto yana da fitattun hanyoyi biyu da masu kirkirar manhaja ke amfani da su, hakan zai sanya kamfanin ya jawo hankulansu don aiki tare da kuma bunkasa hanyar samun kudin shiga.

Your browser doesn’t support HTML5

Google Zata Taimakawa Masu Kirkirar Fasahar Manhajar Wayoyin Hannu - 1'10"