Kamfanin sadarwar yanar gizo na Google, ya yi gargadin cewa bayanan sirri na ‘yan kasar Australia za su kasance cikin hadari, muddun sai katafaren kamfanin sadarwar na yanar gizo ya biya kudi, saboda daukar labarai da yake yi.
Wata dokar da ake tunanin kafawa, ta bukaci kamfanoni irinsu Google da Facebook, su biya kafafen yada labaran kasar Australia, saboda labaran da wadannan kamfanonin ke yadawa a shafukansu na yanar gizon. An yi daftarin dokar ne a watan jiya, bayan da tattaunawar da ake tsakanin gwamnatin Australia da manyan kamfanonin sadarwar yanar gizo biyu ta cije.
A wata wasikar da ta wallafa a shafin yanar gizo yau dinnan Litini, Shugabar kamfanin Google ta shiyyar Australia da New Zealand, Melanie Silva, ta ce za a mika bayanan sirri na ‘yan Australia ga manyan kamfanonin yada labarai, wanda hakan zai taimaka masu wajen saukin tattara karin bayanai.
Google Ya Ce Bayanan Sirri Na 'Yan Australia Za Su Kasance Cikin Hadari Idan Aka Caje Shi
WASHINGTON, D.C —