Google Ta Fitar Da Wani Na’urar Sarrafa Komputa Mafi Sauri A Duniya

Google

Kamfanin Google yace ya cimma wata gagarumar nasara a wani bincike da ya gudanar da ya fito da na’urar sarrafa kopmuta da ake kira “Quantum Computer” mai aiki cikin gaggawa fiye da ainihin komputa da aka saba aiki da ita.

Hakan dai na nufin, lissafin da Quantum Computer zata yi cikin dakikai kalilan, komputa na yanzu zata kwashe dubban shekaru kafin tayi irin wannan aiki.

Quantum computer zata iya yin aiki mai tarin yawa a cikin rana daya kuma a lokaci guda, wanda zai dauki shekara da shekaru kafin komputer ta yanzu tayi irin wannan aiki, ciki har da neman sababbin magunguna da kuma birane da damar tsara bulaguro.

Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar kimiya ta Nature a jiya Laraba, ya nuna Quantum nada tsananin gudu da saurin aiki a duniyar fasaha kana babu wasu dokoki dake hana wannan na’ura komputa aiki, a cewar rubutun masu binciken.

Quantum sabon na’urar komputa ne mai inganci kuma ya kan rikitar a fannin fasaha saboda saurin tantance bayanai. Quantum dai zata iya killace duk wasu bangarori, lamarin da zai dauki komputa na yanzu shekara da shekaru, ciki har da neman sababbin magunguna da kuma birane da damar tsara bulaguro.