Gombe United ta Sallami 'Yan Wasa 10

Gombe United

Hukumar gudanarwa na kungiyar kwallon kafar Gombe United, dake jihar Gombe a tarayyar Najeriya, ta sallami wasu ‘yan wasanta har su goma.

Wadanda ya shafa sune mai tsaron raga na kungiyar mai suna Chinedu kawawa, Obinna Akuchie, mai tsaron baya na gefen hagun sai Douglas Uzama, mai tsaron baya na tsakiya da Shehu Maijama'a.

Sauran sun hada da Demeron Efevwie, da kuma ‘yan wasan gaba su ukku Tasiu Mohammed, Alaba Johnson, Nianna Orji, tare da Shuaibu Ahmadu.

Hukumar Gudanarwar ta yaba da kuma godiya ga ‘yan wasan da aka sallama bisa kwazo da kwarewar da kuma sadaukar da kansu wajan ganin kungiyar ta samu nasara a lokacin da suke takawa kungiyar leda, ta kuma yi masu fatan alheri a duk inda suka koma.

Ta bakin jami'in watsa labarai na Kungiyar Tanimu Umar, ya kara da cewa saukewar ya biyo bayan rahoton da suka samu daga wajan bangaren kwamiti masu horar da ‘yan wasan (Technical Committees ) ya kuma ce wannan na farko ne za'a sake wata sallamar kashi na biyu, ya ce anyi haka ne domin shirye shiryen fuskantar wasan firimiya lig na Najeriya, na 2017.

Har ila yau hukumar ta Gombe united, ta rushe jagororin kungiyan magoya baya ta Gombe united inda ta nada mutane goma sha hudu a mazaunin kwamitin roko wadanda aka nada sune, Anas Adamu, a matsayin shugaba sai Salisu Shuaibu a matsayin magatakarda Abdullahi Umar a matsayin mai bada shawara da kuma Ramatu Yerlele a matsayin shugaba mata tare da wasu mutane goma wadanda suke a matsayin mambobin kungiyar magoya bayan.

Anyi kira ga wadanda aka baiwa rokon da su zamo masu rikon gaskiya har zuwa lokacin da za'a gudanar da zaben shuwagabanni
Gombe united dai ta shafe shekaru biyu bata cikin gasar firimiya lig na Najeriya, sai wannan karon ta samu damar koma ga firimiya lig.