A yayin da ake shiye shiryen fara gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka na 'yan kasa da shekaru 17 wanda za'ayi a kasar Tanzaniya, tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya ta ‘yan kasa da shekaru 17 (Golden Eaglets) ta bar Abuja zuwa kasar Tanzaniya.
Wannan gasa shine karo na 13 da zai fara gudana ranar 14 zuwa 28 ga watan Afirilun 2019.
kungiyar ta Golden Eaglets dake Najeriya ta samu tikitin zuwa Tanzaniyar ne bayan nasara da ta samu a gasar kasashen yammacin Afrika WAFU, cikin watan Satumbar bara wanda ya gudana a Jamhuriyar Nijar, inda ta lallasa kasar Ghana da kwallaye 3 da 1 a wasan karshe.
Tawagar Golden Eaglets ta halarci irin wannan gasar har sau 9 kenan, ta kuma samu nasarar lashe 2 a shekarar 2001 da kuma 2007 tana cikin kasashen Afrika 4 da za su wakilcita a fafata na gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 wacce kasar Brazil za ta karbi bakonci.
'Yan tawagar Golden Eaglets suna rukunin A, tare da masu masaukin baki Tanzaniya da Uganda sai kuma kasar Angola ranar lahadi 14 ga wata za'a bude gasar tsakanin Najeriya da Tanzaniya da misalin karfe biyu na rana agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.