Gobe Labara idan Mai Duka ya kai mu ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki zuwa kasar Kamaru wadda, kamar Najeriya, ‘yan Boko Haram ke kai wa hare-hare ita ma, don tattaunawa da takwaran aikinsa na kamarun Mr Paul Biya a wani yunkuri na hadin gwiwa don yaki da kungiyar ta Boko Haram, wadda ke addabar kasashen.
Shugaban Najeriyan zai kai ziyarar aikin ne bisa rakiyar gwamnonin jahohin da matsalar Boko Haram ke shafa, wadanda jahohi ne da ke makwabtaka da kasar Kamarun wato, Adamawa da Borno. Gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, wanda ya tabbatar ma wakilinmu na jahar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz shirinsu na kai wannan ziyarar, ya kuma kara tabbatar da shirin neman hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Kamaru, ya na kuma kira ga Shugaban Najeriya da ya gina hanyoyi a wasu sassan jahar da ke daura da kan iyakar Kamaru saboda a samu saukin zirga-zirgar tabbatar da tsaro.
Gwamna Jibrilla ya ce banda taimakawa wajen yaki da Boko Haram, hanyoyin za su taimaka wajen kasuwanci da harkokin yau da kullum na mutanen yankin. ‘Yan yankin irinsu Dr. Umar Duhu, dan Karamar Hukumar Madagali, na maraba lale da wannan ziyarar da kuma matakan da ake shirin daukawa na bai daya tsakanin makwabtan kasashen. Haka kuma sun yaba da alkawarin Amurka da Bankin Duniya na ba da tallafin sama da dala biliyan biyu don farfado da yankin na arewa maso gabashin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5