A cewar hukumar zaben jihar Kaduna gobarar da ta tashi a ofishinta ba zata hana yin zabe ba.
Gobarar ta lalata wasu kaya da suka hada da wasu naurori amma hukumar zata gudanar da zaben kananan hukumomi ba tare da yin anfani da naurar dake tantance mutane da aka sani da suna “CARD READER” ba
Shugabar hukumar zabe ta jihar Dr. Saratu Binta Audu Dikko ta yiwa Muryar Amurka bayani akan shirye-shiryen da suka yi. A cewarta gobarar da aka yi a ofishinsu ranar Asabar da ta gabata ta sa sun rasa abubuwa da yawa. Naurorin da suka shirya zasu yi anfani dasu a lokacin zabe sun kone. Amma suna da isassun naurorin da zasu yi anfani dasu. Saboda haka zasu ci gaba da zaben.
Dr. Saratu ta musanta zargin da jam’iyyun adawa suka yi na cewa hukumar bata da kundun rajistan masu zabe. Ta ce suna da ita. Wuta bata tabasu ba.
Sabuwar naurar da zasu yi anfani da ita zata fitar da sakamakon zaben da aka yi a kowane wuri kuma kowa zai gani. Za’a bada sakamakon zabe a kowace gunduma ba sai an kai Kaduna ba. Haka kuma za’a baiyana sunan wanda ya zama shugaban hukumar, a kowace karamar hukuma.
Duk da wannan bayani data yi, kungiyar gamayyar jam’iyyun adawa na cewa akwai lauje cikin nadi tunda za’a yi zabe ba tare da yin anfani da Card Reader ba.
Alhaji Umar Ibrahim shugaban jam’iyyar Labor kuma shugaban gamayyar kungiyoyin adawa na jihar yace yin zabe ba tare da Card Reader ba hankali ba zai dauka ba
Kawo yanzu jam’iyyu sama da 25 ne zasu shiga zaben.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5